Mun ci ribar tallafin noma a Najeriya – Sarkin Dukku

An wallafa

Larsa hoton sama domin kallon bidiyon

Gwamnatin Najeriya ta fito da tsare-tsare da dama na bunkasar harkar noma ta hannun babban bankin kasar CBN.

Tun shekarar 2015 gwamnatin ta kaddamar da tsarin bai wa manona rancen kayan aikin noma, su kuma su biya da amfanin da suka girbe.

A farko an fara shirin ne da noman shinkafa, amma daga baya an fadada zuwa noman masara.

Sai dai wata matsalar da ake fuskanta ita ce yadda wasu manoman suke kin biyan bashin da aka ba su. Amma duk da haka wasu masu rike da sarautar gargajiya da suka shiga shirin na cewa yana da matukar amfani.

Mai Martaba Sarkin Dukku Alhaji Haruna Rashid na biyu, na daga cikin wadanda suka karbi rancen kayan noman masara karkashin shirin.