Tsohuwa mai shekara 100 da ba ta shirya barin aikinta ba

An wallafa

Ku latsa hoton da ke sama don kallon biidyon:

“Na kasa yarda cewa na yi shekara 100, amma fa haka din ne."

Har yanzu Beryl tana aikinta a matsayin mai karbar a wani kantin shan shayi a Ingila.

Ta fara aikin ne shekara 18 da suka wuce lokacin da mijinta ya rasu.

Kuma baya ga wannan aikin tana wasu ayyukan sa kai da dama a asar.