Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda yara ke cin kuruciyarsu a gidajen yari a Kenya
An wallafa
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Ƙasashe da dama a faɗin duniya kan bar yara su zauna tare da iyayensu a gidajen yari.
Sai dai batun na cike da ce-ce-ku-ce, saboda wasu na ganin cewa gidan yari bai dace da zaman yara ba.
A Kenya, ku san yara 200 ne a yanzu haka suke rayuwa a gidajen yari tare da iyayensu mata, abin da ke jawo muhawara a ƙasar kan abin da ya fi kamata a yi don taimakon rayuwarsu.
Wakiliyar BBC Agnes Penda ta yi mana duba kan batun a wannan bidiyon.