Mutumin da ya haddace karin magana da salon magana da ke cikin ƙamus din Turanci na Oxford

An wallafa

Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon:

Shafiu Adamu ya shaida wa BBC cewa daga 1996 zuwa yanzu ya haddace karin magana da salon magana na turanci guda dubu goma.

Ya kara da cewa yanzu haka yana da Kamus na Larabci inda yake kokarin haddace su.

Shafiu Adamu ya ce babban burinsa shi ne a saka shi a kundin Guiness World Book.