Yadda aka yi amfani da fasahar kwamfuta don gano cikin gawar wani Fir'auna

An wallafa

Ku latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon:

A karon farko an yi nazari kan gawar Fir'auna wacce aka adana a Masar bayan an yi amfani da fasahar kwamfuta wajen "bude ta."

Gawar Fir'auna Amenhotep na I wadda aka adana, an gano ta ne a yankin Deir el-Bahari shekara 140 da suka gabata. Sai dai masana ilimi kofai sun kaucewa bude gawar da hannu da zummar kare takunkumi da bandejin da aka rufe ta da su.

Hoton cikin jikin mutum ya nuna wasu bayanai game da fir'auna da yadda aka binne shi da a baya ba a da su.