Ku San Malamanku tare da Ustaz Aliyu Rasheed Makarfi

An wallafa

Latsa hoton sama domin kallon bidiyon

Wani Malamin addinin Musulunci a jihar Kaduna da ke Najeriya Ustaz Aliyu Rasheed Makarfi ya ce babban abin da ya so shi ne haɗin kan al'umma, musamman da waɗanda ba musulmai ba.

Ya ce mutunta kowa da addininsa da mutuncinsa zai taimaka kwarai da gaske wajen samun ji gaba.

''Na farko a addinance, addinin da nake yi na Musulunci idan zama ya hada mu da wadanda ba Musulmai ba akwai buƙatar zaman lafiya,'' in ji Sheikh Aliyu.

Ya ƙara da cewa babu abin da yake faranta masa kamar ganin iyali suna zaman lafiya a tsakaninsu, ko ganin abota ta amana.

"Babu abin da ke yi min daɗi illa ganin jama'a sun taso cikin haɗin kai, duk lokacin da na ga wani ya zo ya wuce da iyalinsa ko a kasuwa ko a shago ko masallaci, a rai na na kan yi farin ciki har na kan yi musu addu'a,'' in ji malamin.

Amma kuma akwai abubuwa da malamin ya ce suna ɓata masa rai, kamar ya ga ana cin mutuncin wani, ko ana son tozarta wani.