Zamantakewa: Hana aure saboda bambancin yare 'rashin wayewar addini ne'

An wallafa

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Zamantakewa shiri ne na BBC Hausa da ke lalubo mafita kan yanayin zamantakewar mutane a bangarori daban-daban.

A wannan kashi na 23 din, shirin ya yi duba ne kan abin da ya sa wasu iyayen ke hana ƴaƴansu auren waɗanda suke da bambancin yare.

Watakila bayan suka da ƙage da maganganun matsin lamba da ta sha fuskanta daga wajen al'umma kan jinkirin aure da ta samu wataƙila ma duk ba a kan hakkinta ba, a karshe Allah Ya kawo mata miji wanda suka yarda da juna da son yin aure.

Ta gabatar da shi ga iyaye da ƴan uwa da abokan arziki, amma sai me? Sai kawai aka fara ce mata kina Hausa Fulani, me za ki yi da ƙabila, me za ki yi da wanda ba yarenku daya ba?

A wasu lokutan ma har iyaye su ce ba za su sa albarka ba saboda bambanci yare.

Shirin zamantakewa na wannan makon ya yi duba ne a kan wannan batu inda muka tattauna da Dr Zahra'u Umar, kwamishinar mata ta jihar Kano, da kuma Aisha Falke mai shafin Northern Hibiscucc a Instagram da Facebook

Asiha Falke ce malamar ajin Northern Hibiscuss a social media, shafin da ke cikin wadanda aka fi yawan kai ƙorafe-ƙorafen zamantakewa, ta ce min matsalar ƙabilanci na daga cikin wacce aka fi kai ƙorafi a kanta.

Dakta Zahra'au Umar malamar addinin Musulunci kuma kwamishinar mata ta jihar Kano ta ce rashin wayewar addini ce ke jawo wannan ja-in-jar.

Malamar ajin northern Hibiscuss sai da ta ja mu har cikin irin dalilan da a ganinta ke sa wasu matan suka fi son auren yaren da ba nasu ba a wannan zamanin.

To ko mece ce masalaha?

Malama Zahra'u ta ce kamata ya yi da iyayen da ƴaƴan duk su duƙufa addu;ar neman zaɓin Allah, idan zuciyar ɗaya ta yi ya sanyi, to ya bar ala,arin kawai a yi shi tun da addini bai hana ba.

Tabbas muna bukatar yarda da juna da amincewa da juna a matsayinmu na ƴan adam, nuna ƙabilanci abu ne da ake adawa da shi a ko ina a fadin duniya.

Kuma ƙwararru ma kan ce al'ummomi suna ci gaba ne idan suna samun cakuduwa tsakaninsu da wasu al'ummomin.

Daina nuna ƙabilanci, zai taka muhimmiyar rawa wajen kyautata zamantakewarmu.