Zamantakewa: Me ya sa wasu mazan ba sa son su ga matansu sun hade musu kai?

An wallafa

Zamantakewa shiri ne na BBC Hausa da ke lalubo mafita kan yanayin zamantakewar mutane a bangarori daban-daban.

A wannan kashi na 22 din, shirin ya yi duba ne kan abin da ya sa wasu mazan ke nuna damuwa idan suka ga matansu sun hade kai

Wani batu na zamanatakewa shi ne na yadda wasu mazan da suke da mace fiye da daya ke shiga cikin damuwa da tasku a duk lokacin da suka lura matan sun hade musu kai.

Shin wannan lamari akwai bukatar ya dame su kuwa?

Wasu ma sun ce to a binciki namiji mai irin wannan halin.

Yayin da wani ke tsoron a hade masa kai, wani kuwa yana can nema yake a hade kan a nasa gidan ko don ya samu kwanciyar hankali. Bari mu ji garabasar da ke cikin hadin kan mata.

Malam Nasiru Ammani Gwarzo da Malama Husnah Kamshi su ne bakin da shirin ya ji ta bakinsu a wannan makon.