Bidiyon da suka shafi Musulunci na cikin mafiya shahara a Tiktok

An wallafa

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Addinai na samun karbuwa a wajen mutane a shafukan sada zumunta.

Daga malaman addinin Kirista mata masu tashe a shafukan sada zumunta, zuwa ga limamai da sauran shugabannin addinai masu wa'azi a Instagram.

Sannan yanzu, wani bincike da BBC ta Ƙaddamar ya nuna cewa musamman ma a Tiktok, bidiyon da suka shafi addini na samun karuwa sosai.