Yadda matasa ke rayuwa babu wayar sadarwa da intanet a Kaduna

An wallafa

Latsa hoton sama domin kallon bidiyon rayuwar matasa babu wayar sadarwa a wasu sassan Kaduna

Ko kun taba tunanin yadda rayuwa za ta iya kasancewa a zamanin nan idan aka ce babu hanyar sadarwa ta zamani bayan da ta riga ta zama jiki ga yawancin jama'a? Misali amfani da wayar hannu da shiga shafukan intanet.

To irin yanayin da al’ummomi da dama suka samu kansu kenan a ciki a yankin arewacin Najeriya sakamakon matsalolin tsaro.

Amfani da hanyoyin sadarwa na zamani na da muhimmanci a irin wadannan wuraren, saboda harkokin kasuwanci da zamantakewa.

To sai dai a yanzu mutanen wasu yankuna a jihar Kaduna kamar takwarorinsu a wasu wuraren sun rasa duka wadannan damammakin, saboda katse hanyoyin sadarwa da gwamnatin jihar Kadunar ta yi a yunkurin dakile matsalar rashin tsaro, matakin da matasan yankin suka ce ya mayar da su baya shekaru aru-aru.

Ba wai yankin mararrabar Jos da ke Kaduna ne kadai matakin na gwamnatin Kaduna ya shafa ba, domin ya shafi sassa da dama na jihar da suka hada da yankin Rigasa na cikin gari, kamar yadda lamarin yake a kafatanin jihar Zamfara in ban da babban birnin jihar, Gusau, da sassa da dama na jihar Sokoto da Katsina da ma jihar Neja.

Hukumomin dai sun ce sun dauki matakin ne domin katse hanzarin masu garkuwa da mutane da hana su tuntubar dangin wadanda aka sace, da kuma hana su samun bayanai daga mutanen da ke tsegunta musu bayanai, musamman idan jami'an tsaro suna son yi musu dirar-mikiya.