Alhaji Adamu Baba Yunusa: Ba za mu bari sha'anin tsaro ya tabarbare a Abuja ba

An wallafa

Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon:

Mai martaba Sarkin Abaji, wanda shi ne shugaban majalisar sarakunan gargajiya na Abuja, babban birnin Najeriya, Alhaji Adamu Baba Yunusa ya ce ba za su taba zura ido sha’anin tsaron birnin ya tabarbare ba.

“Mu sarakan Abuja muna yin taro a kowane wata inda kuma muke komawa garuruwanmu um tattara malaman addini da manoma domin samo bakin yadda za a warware wannan matsala”, in ji Sarkin Abaji.

Sarkin mai lakabin Ona na Abaji ya kara da cewa sabanin sauran jihohi inda ake samun masu rike da sarautun gargajiya da hannu a al’amarin satar jama’a, “mu a nan Abuja babu mai sarautar da zai hada kai da ‘yan ta’adda."

Dangane kuma da mutanen da ke tsegunta wa masu garkuwa halin da jama’a ke ciki, Onan na Abaji ya ce “tuni muka yi magani masu tsegunta wa barayin daji ta hanyar shigar da al’umma cikin sha’anin tsaro.”

Karamar hukumar Abaji dai wadda daya ce daga cikin kananan hukumomin birnin tarayya guda shida, ta yi iyaka da manyan dazuka da ke jihohin Kogi da Nassarawa da Naija.

Masu sharhi dai na ganin idan har ba a yi wa barayin na daji hayaki ba a maboyarsu to akwai fargabar za su iya ci gaba da yin sari-ka-noke.

A yanzu dai karamar hukumar Kwali mai makwabtaka na fuskantar wannan matsala ta masu garkuwa da jama’a.