Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Salon motsa jiki da tsaftar muhalli da ake yayi a jami'o'in Najeriya
An wallafa
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Matasa a Najeriya suna ta bin sahu wajen yi wani sabon abu da ake kira ‘plogging’ wanda ya haɗa motsa jiki da kuma tsaftar muhalli.
Wani ɗalibin jami'a Adeyemi Joy Ifeoluwa, ya bi sahun sarar “plogging” a watan Maris, bayan gano lamarin a wani zauren WhatsApp.
A shekarar 2016 aka fara Plogging a Sweden kuma yana ci gaba da samun karɓuwa a faɗin duniya a ƙasashe irin su Birtaniya da Amurka da Indiya da Sifaniya da kuma wasu ƙasashen Afirka kamar Afirka ta Kudu da Aljeriya da kuma Ghana.
Najeriya na daga cikin manyan ƙasashen Afirka da ake zubar da shara.