Dattijuwar da ke noma yawancin abincinta a gidanta a Abuja

An wallafa

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Hajiya Yalwa dattijuwa ce mai kimanin shekara 80 a duniya wacce take zaune a gidanta da ke babban birnin Najeriya Abuja, ta ce ta rungumi noma ne kimanin shekara 30 da ta gabata.

Gidanta ya zame mata wata gona da take shuka kusan dukkan nau'ukan kayan lambun da take bukata har ma wadanda ake ganin zai yi wuya a ce ana shuka su a inda take.

Ta ce aikin noman da take yi yana ba ta nishadi, yana debe mata kewa sannan yana taimaka mata wajen motsa jiki, da ya sa ba ta takwarkwashe ba duk da yawan shekarunta.