Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Bidiyon yadda ƴan Toungo suka magancewa kansu matsalar masu satar mutane
An wallafa
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Karamar Hukumar Toungo dake jihar Adamawa na cikin irin wadannan yankuna inda kungiyar sintiri ta 'yan banga ta mike tsaye domin kare yankin wanda a shekarun baya ya sha fama da matsalar garkuwa da mutane.
Abokin aikinmu Salihu Adamu Usman ya bi tawagar 'yan sintirin yayin da suke aikin kare garinsu kuma sun yi amfani da babura masu kafa biyu wajen zuwa kauyuka dake tsakanin Najeriya da jamhuriyar Kamaru inda daga can ne masu satar mutanen ke shigowa cikin garin Toungo.
Tsara bidiyo: Salihu Adamu Usman
Tacewa: Bashir Idris