Khaby Lame: Sirrin nasarar dan Afrikan da ke da mabiya miliyan 51 a Tiktok

An wallafa

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Wani dan kasar Senegal kuma mai tashe a shafin Tiktok Khaby Lameya zama shahararre.

An san shi sosai da halayyarsa ta dakile camfe-camfen da suka baibaye rayuwar mutane da yawan ɗaga kafaɗa da yake yi, nan da nan sai ya zama sananne a gidaje da dama a fadin duniya.

Matashin mai shekara 21 a yanzu yana aikin hadin gwiwa da fitattu irin su Naomi Campbell da Greta Thunberg, kuma shi ne mutum na biyu mafi tashe a shafin Tiktok.

Amma ta yaya ya shahara da sauri haka, kuma me masoyansa a Senengal ke cewa?