Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda ake cin babbar kasuwar doya ta garin Ganye a Adamawa
Latsa hoton sama domin kallon bidiyon:
Kasuwar doya ta garin Ganye da ke jihar Adamawa a arewa maso gabashin Najeriya kasuwa ce da ke taka muhimmiyar rawa wajen samarwa kasar da ma kasashe makwbata doya.
Da zarar kakar doya ta yi masu sayenta daga wurare daban-daban na fara zuwa garin na Ganye daga ranar Talata duk da cewa sai asabar kasuwar ke ci.
A ‘yan shekarun baya-bayan nan dai Najeriya ta fara fitar da doya kasashen ketare a hukumance a wani mataki na lalubo sabbin hanyoyin kudin shiga maimakon dogaro kacokan ga man fetur.
A ko wane mako ana ciniki na miliyoyin naira kuma akwai masu zuwa sari daga yankuna daban-daban.