Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda fara take rufa wa mutane asiri a jihar Borno
An wallafa
Latsa hoton da ke sama domin kallon wannan bidiyon
Dubban mutane suka dogara da sana'ar kama fara da sayar da ita a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya.
Mafi yawan masu wannan sana'a dai mata ne da suke saya daga mutanen da suka kamata a cikin daji, sannan su soya su kuma su sayar da ita ga jama'ar jihar.
Mutan Borno sun dauki fara a matsayin wani abincin marmari da mata da maza da yara da manya suke ci.
Bidiyo da tacewa: Yusuf Ibrahim Yakasai