Matan auren da suke saɓa al’ada a shafukan sada zumunta a Indiya

An wallafa

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

A lokacin da take yarinya, Pradnya na son wani wasa da ake yi a Indiya mai suna kabaddi. Amma duk da cewa ta iya wasan sosai, iyayenta ba su taɓa goyon bayan burinta ba.

Sai dai yanzu da take da shekara 47 kuma mijinta ya rasu, ta ce ta gano abin da take tsananin so - wato rawa.

Kuma godiya ga shafukan sada zumunta, ita ma Vasanti mai shekara 65 a baya ta sha fafutukar tallan kayan taɓa-ka-lashe a wulbaro.

Amma a yanzu ƴaƴanta maza uku suna da ayyukan yi masu ƙwari, kuma ta fara yaɗa hotunanta na yadda take kwaikwayon fitattun waƙoƙi.