Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Bidiyo: Masu bincike sun leka 'Kogon Jahannama mai tarin aljanu' a Yemen
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Wata tawagar masu bincike daga Oman sun yi wani kokari da ba a taba zaton zai faru ba na zama mutane na farko da suka shiga kogon da aka fi kiransa da "Kogon Jahannama" - da ke can yankin sahara a kasar Yemen.
Mazauna yankin sun dade suna tsoro da gudun kogon da ake kira Well of Barhout - mai zurfin mita 112 da fadin mita 30.
An shafe daruruwan shekaru ana yada camfin cewa nan ne matattarar aljanun duniya.
Sai dai tawagar masu binciken sun gano duwatsun alfarma da ma'adinai da tarin shuri, wadanda suka samu sakamakon ruwan da ke diga a ciki.
Kazalika sun ci karo da macizai da mushen dabbobi da tsuntsaye wadanda suka sa kogon ke wani irin wari marar dadi.
HAKKIN MALLAKA: AFP MUSIC