Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Bidiyo: Rakuma masu nunkaya a ruwa na barazanar karewa
An wallafa
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Rakuman Kharai wasu nau'i ne da ke wani yanki da ake samun gishiri a kogi a yammacin jihar Gujarat na India.
Suna iya ninkaya a kogi mara zurfi sosai don isa dajin da za su samu ciyawar kiwo.
Amma makiyaya sun ce harkar samar da gishiri yana sa yankuna masu tsirran na bushewa, kuma hakan na yi wa rayuwar rakuman barazana.