Coronavirus: Rayuwa a sansanin 'yan bautar kasa zamanin annobar korona

An wallafa

Ku latsa wannan alamar hoton da ke sama domin kallon bidiyo

Kusan za a iya cewa sansanin 'yan bautar kasa shi ne wani wuri da yake da yawan matasa a lokacin zaman wurin na tsawon makonni.

Tun dai bayan barkewar annobar korona, ake ta nazarin yadda rayuwar masu bautar kasa za ta kasance a sansaninsu.

A baya ma dai an rufe sansanonin inda har ta kai ga dage yi wa kasar hidima lokacin da annobar ke kan ganiyarta kamar dai yadda al'amura suka tsaya cik a fadin duniya.

A bana wadda ita ce karo na shida da ake bai wa masu bautar kasa horo tun bayan bullar annobar korona, BBC ta leka sansanin masu yi wa kasa hidima da ke Kubwa Abuja domin ganin yadda rayuwa ke tafiya.