Abin da ya sa salona ya sha bamban da na sauran ma'aikatan BBC - Abdussalam Ibrahim Ahmed

An wallafa

Fitaccen ma'aikacin Sashen Hausa na BBC, Abdussalam Ibrahim Ahmed, ya bayyana yadda ya kwashe fiye da shekara 20 yana aiki a BBC.

Ya bayyana haka ne a wata tattaunawa ta bidiyo.

Ya ce ya kwashe fiye da shekaru 20 yana aiko da rahotanni daga birnin Enugu da ke kudu maso gabashin Najeriya, inda ya soma aiki da kamfanin jaridar Gaskiya Ta Fi Kwabo.

Dan jaridar, wanda yake maganar da harsuna da dama, ya bayyana yadda salonsa ya sha bamban da na sauran ma'aikatan BBC Hausa.