Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Matashin da ke ɗaukar nauyin karatunsa ta hanyar zana hotunan mutane a Kano
An wallafa
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
A yanzu matasa a arewacin Najeriya na zaburowa don magance matsalar neman ilimi ta hanyar samun aikin yi don ɗaukar nauyin karatunsu ba tare da jiran iyayensu sun yi musu ba.
Da yawansu sun gwammace su nemi sana'ar hannu don ɗaukar nauyin kawunansu.
Abbas Nabayi mai shekara 24 na daga cikin irin waɗannan matasa.
Yana zana hotunan mutane da sauran abubuwa, inda yake sayarwa yana amfani da kuɗin wajen ɗaukar nauyin karatunsa.
Yanzu yana karatun samun shaidar NCE ne a Kano.
Ya shaida wa BBC tsare-tsaren da yake yi don inganta rayuwarsa a nan gaba.