Mutum fiye da 2000 ne ke aiki a gonata - Farouk Adamu

An wallafa

Ku latsa wannan alamar hoton da ke sama domin kallon wannan gona

A iya cewa idan akwai mutum daya tilo da za a ce ya amsa kiran gwamnatin tarayya na komawa gona to shi ne Farouk Adamu Aliyu.

Farouk Adamu wanda tsohon dan majalisar tarayya ne kuma jigo a jam'iyyar APC mai mulki ya koma mazabarsa ta Birnin Kudu inda ya bude wannan katafariyar gona mai girman kadada 70.

Wannan gona wadda za a iya cewa ta zamani ita ce irinta ta farko a arewacin Najeriya.

A wannan gona ana kiwon shanu da rakuma da awaki da tumaki da kaji da agwagi da kifi da dai sauransu baya ga katafaren kamfanin yin takin zamani.

Har wa yau, wani abun da ya banbanta wannan gona mai suna Malam Alu Farm da sauran gonaki shi ne noman tumatir na zamani da ake yinsa a cikin daki.

"Na kafa wannan gona ne ba domin samun riba ba sai kawai domin al'ummar da suka fitar da ni kunya su amfana ta hanyar rage musu rashin aikin yi." In ji Farouk Adamu Aliyu