Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Tokyo Olympics 2021: Ƴan tseren da suka je gasar da goyon ƴaƴansu
An wallafa
Ku latsa hoton da ke ƙasa don kallon bidiyon:
A farkon wannan watan ne, masu shirya Gasar Olympics ta Tokyo suka sanar da cewa mata 'yan tsere masu shayarwa na iya tafiya da ƴaƴansu na goye idan suna buƙatar hakan.
Labarin ya sanyaya rayukan uwayen da a baya ke zaɓar ko dai su yaye ƴaƴan su tafi gasar ko kuma su haƙura.
Wakiliyar Sashen Wasanni ta BBC Africa, Michelle Katami, ta tattauna da wasu iyaye mata gwarazan tsere daga Kenya don jin yadda a baya suka dinga haɗa sana'arsu da reno.