Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ranar Abokai Ta Duniya: 'Abota tana sa mutum ya yi tsawon rai'
An wallafa
A duk shekara, an ware ranar 30 ga watan Yuli domin ta kasance Ranar Abota Ta Duniya.
Binciken masana kimiyya ya nuna cewa bukatarmu ta zama da abokai ta zarta duk yadda muke tsamani.
Tarihin halittar dan adam ya nuna cewa bil adama mutum ne da ke son abota.
Wata 'yar jarida kan Kimiyya Lydia Denworth ta yi nazari kan tsarin abota ta hanyar tuntubar masana domin sanin abubuwan da suka gano game da muhimmancin abota.