Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mohamed Bazoum: Ilimi na fuskantar manyan matsaloli a Jamhuriyar Nijar
An wallafa
Shugaban Jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum ya ce kasarsa tana fuskantar manyan matsaloli ta fuskar samar da ilimi.
Ya bayyana haka ne a yayin da ake soma wani babban taro a birnin London kan yadda za a bunaksa ilimi a kasashen duniya.
Gwamnatin Birtaniya da ta Kenya ne suke daukar nauyin taron.
Shugaba Bazoum ya ce daya daga cikin manyan matsalolin da ilimin 'ya'ya mata yake fuskanta shi ne yadda ake korar su daga makarantar.