Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Rawa 'yanci ce - in ji 'yar Najeriya da ke koyar da rawar Afirka a Japan
An wallafa
Latsa hoton sama ku sha kallo
Yinka Oshitelu 'yar Najeriya ce kuma mai fasfon Birtaniya amma mazauniyar Tokyo na Japan.
Tana cikin masu koyar da yara rawar Afirka ta salon hip hop a makarantarta da ke Tokyo.
Tana taƙama gami da alfahari da abin da take yi, tana mai cewa rawa ta taimaka mata wajen samun 'yanci da kuma yaƙi da ɗabi'ar zaƙuwa.