Bidiyon yadda aka harba roka shugaban ƙasa na Sallar Idi a Afghanistan

An wallafa

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Shugaban ƙasar Afghanistan na cikin Sallar Idi da sauran al'umma sai aka harba rokoki a kusa da fadar gwamnatin.

Sai dai duk da ƙarar fashewar da aka ji Shugaba Ashraf Ghani da sauran manyan jami'an gwamnati sun ci gaba da sallarsu cikin nutsuwa.

An ji karar fashewar a talabijin yayin da ake watsa yadda ake gudanar da sallar kai tsaye.

Wannan hari na zuwa ne makonni bayan tafiyar dakarun Amurka, wdanda suka janye bayan shafe shekara 20 a Afghanistan.