Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Bidiyo: Mutumin da ya kera mota mai amfani da wutar lantarki
Latsa wannan alamar hoton da ke sama domin kallo
Ya'u Mukhtar ya ce ya kera wannan mota mai amfani da wutar lantarki ne sakamakon irin wahalar da masu mota ke shiga wajen neman man mota.
"Abin da ya sa na fara tunanin kera wannan mota shi ne bisa la'akari da yadda masu mota ke fama a lokacin da kungoyi masu dakon mai ke yajin-aiki."
Ya ce yanzu haka dai ya kera motar ne domin hawan mutum biyu kuma zai lullube motar nan gaba kadan.
"Nan ba da jimawa ba za mu kera irin wannan motar mai daukar mutane da dama wato wadda ta fi wannan girma."
Ya'u Mukhtar ya yi amfani da kwanon keke mai kafa uku wajen kera wannan mota.