Jayayya tsakanin kudu da arewa kan mulkin 2023 ba ta da amfani - Bagudu

An wallafa

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

A Najeriya gwamnan jihar Kebbi Abubakar Atiku Bagudu ya ce jayayya tsakanin yankunan kasar kan bangaren da shugabancin kasar zai koma a shekara ta 2023 ba za ta tsinana wa kasar wani abin alheri ba.

A wata tattaunawa ta musamman da Sashen Hausa na BBC, gwamnan ya ce tattaunawa da hadin kai ne suka haifar da zababbun shugabannin kasar da suka gabata, kuma haka din ne kawai zai sa kasar ta iya lalubo shugaba wanda zai kai ta ga tudun mun-tsira.

Amma da farko Haruna Ibrahim Kakangi ya tambayi gwamnan game da inda aka kwana wajen ceto daliban makarantar sakandaren gwamnati ta garin Yawuri wadanda ‘yan fashin daji suka sace a jihar ta Kebbi.