Bidiyon shirin Zamantakewa: Shawarwari ga namiji mai mace fiye da ɗaya

An wallafa

Ku latsa hoton sama don kallon bidiyon:

Zamantakewa shiri ne na BBC Hausa da zai dinga lalubo mafita kan yanayin zamantakewar mutane a bangarori daban-daban.

A wannan kashi na huɗun, shirin ya yi duba ne kan rayuwar namiji mai mace fiye da ɗaya, da irin adalcin da ya kamata ya shimfiɗa a tsakanin iyalansa da yadda zai kyautata zamantakewarsa da su don a zamu kwanciyar hankali.