Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Bidiyo: Ina mafita kan sace-sacen ɗalibai a makarantun Najeriya?
An wallafa
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
A wannan bidiyo, Abdulbaƙi Jari ya yi duba kan batun satar ɗalibai da yake neman zama ruwan dare gama duniya a arewacin Najeriya.
Daga watan Disamban 2020 zuwa yanzu an ƙiyasta cewa ƴan bindiga sun sace ɗalibai sama da 1,000 a jihohin Katsina da Kebbi da Neja da Kaduna da kuma Zamfara.
Sai dai tuni an ceto wasu yayin da har yanzu wasu ke hannun ƴan bindigar.