Abin da ya janyo matsanancin karancin wutar lantarki a Abuja

An wallafa

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Tun cikin watannin farko na wannan shekarar ne mazauna Abuja, birnin tarayyar Najeriya ke koka wa kan tabarbarewar samun wutar lantarki.

Abin da ke matukar illa ga sana’o’I da sauran harkoki na yau da kullum.

Wannan ya kara tilasta wa al’umma yin amfani da na’urorin samar da wuta na janareto.

Mun tuntubi Injiniya Danliti Inusa, shugaban bangaren kula da samar da wutar lantarki na kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja (AEDC), wanda ya yi bayani kan dalilan da suka haifar da matsalar karancin wutar da ake fuskanta a yankin na Abuja.