NITDA: Yadda WhatsApp ke ɗaukar bayanai da Illar amfani da VPN - Kashifu Inuwa Abdullahi

An wallafa

Latsa hoton sama domin kallon bidiyon

Gwamnatin Najeriya ta ce tana ci gaba da tattaunawa da kamfanin sada zumunta na WhatsApp kan sauye-sauye da kamfanin ya yi dangane da amfani da bayanan masu aiki da WhatsApp din a kwanakin baya.

Gwamnatin ta ce tana ɗaukar wannan matakin ne domin kare al'ummarta daga cutarwar intanet.

Wannan na zuwa ne bayan shafe makwanni da dakatar da shafin Twitter a ƙasar.

BBC ta tattauna da Kashifu Inuwa Abdullahi, shugaban hukumar bunƙasa fasahar zamani ta Najeriya NITDA game da batun da kuma ayyukanta.