Sarkin Kano Aminu Ado Bayero: Babban burina a rayuwa ya cika

An wallafa

Latsa hoton sama ku kalli bidiyo:

Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya ce babban burinsa a rayuwa shi ne ya gaji magabatansa kuma yanzu hakan ya tabbata.

Cikin wannan hira ta musamman da ya yi da BBC Hausa, sarkin ya ce baya ga murnar gadar mahaifinsa da yake yi yana kuma murnar zaɓarsa da Allah ya yi domin ɗora masa nauyin taimaka wa al'ummarsa.

Ya bayyana haka ne yayin da ake shirin bikin ba shi sandar girma, yana mai cewa a halin yanzu murna biyu yake yi.

Kazalika sarkin ya bayyana cewa babu wata tashin jituwa tsakanin 'yan gidan sarautar Kano.

A cewarsa a al'adance duk wanda ya nemi wani abu bai samu ba ba zai ji dadi ba amma hakan ba ya nufin akwai rashin matsala tsakaninsa da wadanda ya gada da wadanda suka nemi mulki tare.