Ra'ayoyin wasu ƴan Kano kan sauya kundin mulkin Najeriya na 1999

An wallafa

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Ƴan majalisar wakilan Najeriya na ci gaba da sauraren ra’ayoyin al’umma kan irin gyaran fuskar da suke bukatar a yi wa kundin tsarin mulkin kasar, da za a shafe kwanaki biyu ana yi.

Batutuwa da zaman dai ya fi mayar da hanakali shi ne batun ƙirƙiro sabbin jihohi da batun sakarwa ƙananan hukumomoi da ɓangaren shari'a mara don su tsaya da ƙafafuwansu.

Jihar Kano na daya daga cikin shiyyoyin da majalisar wakilan Najeriyar ta waren don za ai wannan zama na tsahon kwanaki biyu farawa daga yau.