Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda masu hali ke bai wa jama'a abincin buda-baki a Abuja
Latsa wannan hoton da ke sama domin kallon bidiyon
Mohammed Jammal a bana ma kamar kowacce shekara na zagayawa lungu da sako na birnin tarayya, Abuja domin rarraba abincin bude-baki.
Wani abun ban sha'awa shi ne yadda mai dakin Mohammed ce ke tuka motar da ake amfani da wajen raba abincin mai kirar a-kori-kura.
Jammal ya ce "na ko yi wannan al'ada ne daga wurin mahaifana kuma na kan fara tanadin kudin tunda wuri saboda ka da a samu matsala."
Duk da cewa malamai na kokarin hana jama'a bayyana irin wannan alkairi musamman a kafafen watsa labarai amma Jammal ya ce "na yi hakan ne saboda na kwarara wa sauran jama'a gwiwa."