Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Masar Bauchi: Yadda iyaye ke koya wa 'ya'yansu sana'ar masa
An wallafa
Latsa hoton sama domin kallon bidiyon
Masar Bauchi na daga fitattun abinci a kasar Hausa, wacce kuma take kasancewa tsaraba mai daraja ga duk wanda ya yi tafiya zuwa Bauchi.
Babu cikakken bayani kan takamaimen lokacin da aka fara Masar Bauchi, amma dai akwai gidaje da dama da suka shahara da sana'ar masar.
Masu sana'ar masar suna gadarwa 'ya'yansu da jiokokinsu wannan sana'a.
BBC ta kai ziyara daya daga gidajen da ake sana'ar wainar a unguwar Bakin Kura da ke birnin na Bauchi.