Shin allurar riga-kafin korona tana da illa?

An wallafa

Riga-kafin korona yana taimakawa wajen kare mutane daga fadawa cikin rashin lafiya magashiyan idan suka kamu da cutar.

Amma yaya allurar take aiki? Shin riga-kafin zai sa mutum ya kwanta rashin lafiya?

Marnie Chesterton ta yi karin haske game da yadda riga-kafin korona ba zai sa mutum ya kamu da cutar ba da kuma dalilin da ya sa mutumin da aka yi wa allurar ke fuskantar matasala irin su ciwon kai da zafin jiki.