Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ina jin kunya a ce ni shugaba ne a arewa - Gwamna Bala Muhammad
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Gwamnan jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin Najeriya Sanata Bala Muhammad Abdulkadir, ya ce akwai gazawar shugabanci a arewacin ƙasar, ganin yadda lamura ke kara taɓarɓarewa.
Gwamna Bala ya ce talauci da rashin aikin yi na daga manyan matsalolin da suke addabar arewa da shugabanni suka kasa shawo kansu.
Gwamnan ya kuma yi karin bayani kan kalaman da ya yi kwanakin baya, dangane da dalilan da suka sa Fulani makiyaya ɗaukar bindiga.
Ya ce ba ya goyon bayan aikata laifuka ko kadan, amma dai ya kamata a duba tushen lamarin in har ana so a kawo karshensa.
Ya ce zaluncin da ake yi wa fulani shi ne babban abin da ya sa wasu miyagu daga cikinsu daukar makamai.
Gwamna Bala ya ce akwai hadin bakin wasu sarakuna.
Ɗaukar bidiyo da tacewa: Yusuf Ibrahim Yakasai
Wasu labarai da za ku so ku karanta: