Mutane na taka sayyada a Kano saboda yajin aikin masu adaidaita sahu

An wallafa

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Masu sana'ar tuka babur mai kafa uku na a daidaita sahu ne suka shiga yajin aiki a jihar Kano da ke arewacin Najeriya, kan biyan harajin naira 100 da za su dinga biyan gwamnati kullum.

Hakan dai ya biyo bayan yadda hukumar Karota ta umarci masu sana'ar babur din na adaidaita sahu da su ringa biyan naira dari kullum, wani batu da masu baburan suka nuna adawarsa da shi.

Ga dai bidiyon da BBC Hausa ta dauko na irin yadda birnin ya kasance sakamakon yajin aikin a ranar Litinin.