Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ku San Malamanku tare da Farfesa Mansur Sokoto
An wallafa
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Fitaccen malamin addinin nan a jihar Sokoton Najeriya Sheikh Farfesa Mansur Sokoto ya ce duk da cewa wasanni na daga cikin abin da ya fi so, to ba ya iya yin su a yanzu saboda a Najeriya akwai abubuwa da yawa da ko yana so to ba zai iya yin su ba.
Malamin ya faɗi hakan ne a wata hira ta musamman a shirin Ku San Malamanku na BBC Hausa, inda ya ce a lokacin da yake Sudan da Madina ya yi wasanni da suka haɗa da Takwendo da Kung Fu da Iyo wato Swimming.
Sai dai malam ya ce a yanzu ya kan yi wasu wasannin motsa jiki da suka sauwaƙa a gida.