Mutumin da ya ciyar da maguna 10,000 lokacin kullen korona

An wallafa

Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon:

Lokacin da ake tsaka da dokar kulle a Wuhan a yayin da cutar korona ta barke a kasar China dubban masu maguna ba su iya komawa gida domin ciyar da su ba.

Don haka ne Du Fan, shugaban kungiyar da ke kare kananan dabbobi a Wuhan da abokan aikinsa, suka yunkura wajen ganin sun rika bai wa magunan abincin da suke bukata.