Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Bidiyo: Yayin shan shayin goruba ya ɓulla a Kano
An wallafa
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyo:
Wani sabon yayi da ya ɓullo a jihar Kanon Najeriya shi ne yadda mazauna birnin da dama suka koma shan shayin goruba maimakon irin na sauran ganyen shayi da aka saba da su.
Karbuwar da shayin yake yi ne ma ya sa matasa da yawa fara sana'ar sayar da shi.
Masana lafiya dai na nuna cewa shayin na goruba na da alfanu ga lafiyar dan adam amma kuma ba kowa da kowa ba.
Wakilinmu a Kano Khalifa Shehu Dokaji ya hada mana daga teburin wani mai shayin goruba.
Bidiyo: Khalifa Shehu Dokaji
Tacewa: Yusuf Ibrahim Yakasai