Bidiyon yadda gobara ta cinye wata kasuwa a Abuja

An wallafa

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Gobara ta lashe daruruwan shaguna da rumfuna a kasuwar Tippa Garage dake unguwar Gwarinpa a Abuja babban birnin Najeriya.

Mutum guda ya kuma mutu yayin da yake barci a shagonsa inda ya kone kurmus yayin da gobarar ta tashi cikin dare a jiya Laraba.

Baki dayan ksuwar dai ta kone kurmus.

Dama dai ana sayar da kayakin da suka hada da na abinci, kayan marmari, da tufafi, da kayan gwan-gwan, da kayan gini da dai sauransu.

Shugaban ‘yan kasuwar, Usman Abdullahi, ya shaida wa BBC cewa ko da ya ke kawo yanzu ba a kai ga tantance hakinannin adadin dukiyar da aka yi hasara ba, amma hasarar da za ta iya kia wa ta sama da naira miliyan 300.

Wasu bidiyo da za ku so ku kalla