Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Bidiyon Ku San Malamanku tare da Sheikh Maqari
An wallafa
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Fitacce malamin addinin Musuluncin nan na Najeriya Sheik Ibrahim Ahmad Maqari ya ce babban abin da ya sanya a gaba shi ne samar da makarantu ko zawiyyoyi ko masallatai wadanda za su dace da tsari na wannan karni.
Malamin, wanda shi ne kuma limamin babban masallacin Juma'a na Abuja, ya faɗi hakan ne a hirar da ya yi da BBC Hausa a shirinmu na musamman mai taken ''Ku San Malamanku''.