Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Bidiyon hira da Sheikh Karibullah a shirin Ku San Malamanku
An wallafa
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Shirin Ku San Malamanku na wannan makon ya tattauna ne da Sheikh Karibullah Nasiru Kabara, shugaban ɗariƙar Ƙadiriyya na Afirka.
A cikin shirin Sheikh ya ce yana da gashin Annabin Allah Muhammad SAW a ajiye a wajensa.
Malamin ya faɗi hakan ne a cikin shirin Ku San Malamanku na BBC Hausa, har ma kuma ya nuna wa Yusuf Ibrahim Yakasai gashin.