Ku San Malamanku tare da Sheikh Halliru Maraya

An wallafa

Wani fitaccen malamin addinin Musulunci a jihar Kadunan Najeriya ya ce shi ba ya siyasa, mutane na ganin kamar yana yi ne don kawai ya ta ba riƙe muƙami a gwamnatin farar hula shi ya sa ake ganin kamar shi ɗan siyasa ne.

Malamin ya bayyana hakan ne a hirarsa da BBC Hausa a shirinmu na musamman na Ku San Malamanku, inda ya ce tsohon gwamnan Kaduna marigayi Patrick Yakowa ne ya naɗa shi mataimaki na musamman kan harkokin addini da aikin Hajji.

"Duk da cewa ni ba ɗan jam'iyyarsa ba ce ta PDP. Sannan sai da na sa masa sharuɗɗa sannan ya yarda da hakan.

Malamin haifaffen Unguwar Tudun Wada ne a garin Kaduna, kuma an haife shi ne a watan Agustan 1969, sai dai yana da shekara biyu mahaifiyarsa ta rasu, dalilin da ya sa ya samo sunan maraya kenan.

Ya fara karatun allo tun yana ɗan shekara bakwai, kuma a yanzu shi ne mai gudanarwa a Gidauniyar Zaman Lafiya Ta Duniya a arewacin Najeriya, wato Global Peace Foundation.

Sheikh Maraya ya ce ya fi ƙwarewa a fannonin Fiƙihun Malikiyya da Luggar Larabci da ilimin Hadisi da ilimin Tafsiri da aka fi saninsa a kai.

Ya ce malamansa da ya fi alfahari da su su ne kamar limamin Masallacin Tudun Wadan Kaduna Sheikh Abdulkarim Hashim da marigayi Malam Abubakar Tureta da marigayi Sheikh Lawal Ƙaura Zariya (wanda nake zuwa Zariya kullum tun daga Kaduna donɗaukar karatu a wajensa).