Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Sabbin tsare-tsare uku da gwamnatin Najeriya ta yi wa 'yan gudun hijira
Latsa wannan hoto na sama domin kallon bidiyon tsare-tsaren da aka yi wa 'yan gudun hijra.
Shugaban hukumar 'yan gudun hijra ta Najeriya, Sanata Bashir Garba Muhammad, ya ce yanzu haka ya fito da wasu tsare-tsare guda uku domin inganta rayuwar 'yan gudun hijrar Najeriya.
Ya ce "akwai 'yan gudun hijira miliyan 2.5 da suke cikin Najeriya sakamakokn rikicin Boko Haram da ɓarayin daji, inda kuma mutum kimanin dubu 400 suka ƙetara kasashe masu makwabtaka wato Nijar da Kamaru da Tchadi domin neman mafaka."
Sanata Bashir ya kara da cewa, akwai sansanonin 'yan gudun hijira fiye da 200 a faɗin Najeriya sannan kuma akwai 'yan gudun hijirar da suka shiga cikin al'umma da ba su da ƙididdigarsu.